Buhari Ya Yi Kiran Mayar Da Kasar Mali Saniyar Ware

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi kira ga sauran shugabannin nahiyar Afrika da su tashi haikan domin ganin kasar Mali ta koma cikin hayyacinta.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne yayin da ya ke gabatar da jawabi a wurin taron shugabanni ECOWAS da aka yi ranar Alhamis domin daukan matakan warware rikicin kasar Mali.

Tuni ECOWAS ta sakawa kasar Mali takunkumi tare da bawa sauran kasashen ECOWAS da ke makwabtaka da Mali umarnin su rufe iyakokinsu da kasar har sai sun koma turbar dimokradiyya.

Yayin taron, shugaba Buhari ya bayyana cewa juyin mulkin da sojoji su ka yi a kasar Mali zai shafi batun tsaro da zaman lafiya a yammacin Afrika. “Abinda ya faru a kasar Mali ba kankanin koma baya ba ne da zai iya shafar zaman lafiya da tsaro a kasashen nahiyar Afrika.

“Lokaci ya yi da ya kamata haramtacciyar gwamnatin kasar Mali ta yi abinda ya dace, ta bi kundin tsarin mulki tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar,” a cewar Buhari.

Sannan ya cigaba da cewa; “Najeriya ta goyi bayan shugaban ECOWAS, shugaba Mahamadou Issoufou, a kan daukan tsauraran matakai da zasu gaggauta warware matsalolin da kasar Mali ta shiga.

“Zaman lafiyar kasar Mali yana da matukar muhimmanci ga yankin Afrika ta yamma. Dole mu hada karfinmu wuri guda a matsayin ECOWAS, AU, UN, da sauran ma su ruwa da tsaki har sai mun tabbatar al’amura a kasar Mali sun daidaita, an koma tsarin gwamnati na jama’a.”

Buhari ya gana tare da sauran shugabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2020. Ganawar ta gudana ne ta kafar yanar gizo, kamar yadda shafin fadar shugaban kasa ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Labarai Makamanta