Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Buhari yayi watsi da kudirin Zaben ‘Yar Tinƙe da sauran kwaskwariman da akayiwa dokokin zaben kasar nan. Yace kowace Jam’iyyar siyasa tanada damar yin kalar zaben cikin gida din da take so.
Idan ba a manta ba a ranar 10 ga watan Nuwambar wannan shekara ne Majalisar kasar mu ta sanyawa dokar gyara da kwaskwariman kundin tsarin dokokin zaben kasar nan hannu wanda ta mikawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu domin a fara aiki da sabon tsarin a zaben shekarar 2023.
Sabbinn Canje Canjen da akayi a sabon doktarin dokar zaben da Shugaba Buhari yaki sanyawa hannu sun hada da
1- Soken Zaben Fidda Gwani wanda ake Kira primary election da maye gurbin sa da zaben Yar tinƙe. Saboda mafi yawancin Yan Kasa suna zargin wurin zaben Fidda Gwani anan manyan Yan Jam’iyya ke cusawa mutane yan takarar da basa so a mafi yawancin kujeru.
2- Sai Kuma tura sakamakon zaben ta na’ura mai kwakwalwa ta yadda za a samu saukin satar kayayyakin zabe da sauran kalubalen dake biyo baya yayin zaben ko lokacin tattara sakamakon zaben. Kuma yin anfani da na’ura mai kwakwalwa zai rage makudan kudaden da ake kashewa wurin yin zabe a kasar.
3- Hukumar Zabe Mai zaman kanta na kasa ne zata dinga gudanar da kowane irin zabe a fadin kasar ba kamar yadda ake barwa gwamnonin jihohi suke yin zaben kananan hukumomi ba. da dai sauran dokokin zaben kasar.
Daman ko a makon daya gabata wasu masana harkar siyasa sun bayyana cewa zaiyi wuya shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar nan, a cewar Ambassador Salisu Bala Suleiman Babu wani dalilin da zaisa shugaba buhari ya aikewa hukumar zabe takardar neman shawara kamin shugaban Kasa Wanda akewa lakani da (Commander In Chief) ya Sawa doka hannu.
Tun daga nan nasan zaiyi wuya gwamnonin kasar nan su bar Buhari ya sawa dokar nan hannu domin muddin yasa hannu gwamnoni da dama da Yan majalisu zasu rasa kujerunsu a zaben 2023 domin hakkin zaben shugabanni ya dawo hannun ‘yan Najeriya Kuma hakan ba karamar barazana bane.
Wasu Kuma na ganin Yan Majalisar sunyi haka ne saboda cin kashin da gwamnonin jihohinsu sukai masu a zabukan cikin gida da aka gudanar a fadin kasar.
You must log in to post a comment.