Buhari Ya Yi Bikin Ranar Haihuwar Shi A Turkiyya

Rahotanni dake shigo mana daga birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanka kek ɗin murnar ranar haihuwarsa a Turkiyya bayan ya cika shekara 79 da haihuwa.

An tsara kek ɗin da launin Najeriya wato fari da tsanwa inda bayan ya yanka kek ɗin sai ya tattauna da hadimansa kafin suka tafi wajen taron tattaunawa kan cinikayya tsakanin Turkiyya da ƙasashen Afrika.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai ci gaba da yin iya bakin ƙoƙarinsa wajen yi wa ƴan Najeriya aiki har zuwa lokacin da zai miƙa mulki a 2023.

Shugaban ya kuma ce zai koma gona ne domin ci gaba noma da kiwo bayan ya miƙa mulki.

Labarai Makamanta