CORONA: Buhari Ya Umurci A Rabawa Talakawa Shinkafar Da Hukumar Kwastam Ta Kwace

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumar fasa kwauri ta kasa (custom) data fito da shinkafar da ta kwace hannun masu fasa qwauri domin rarrabawa ‘yan najeriya musamman a halin da suke ciki yanzu na zama a gida.

Majiyar jaridar muryar ‘yanci ta ruwaito mana cewa tuni dai hukumar kwastam ta karbi wannnan umurni kuma zata fara aikewa da kayyyakin abincin zuwa ma’aikatar da ke kula da sha’anin agaji da taimakon gaggawa na kasa.

Tun bayan rufe iyakokin kasar da akayi a shekarar da ta gabata, hukumar kwastam ta kwace shinkafa mai tarin yawa, inda dama ‘yan kasa na ta kiraye kiraye ga gwamnatin data fito dashi domin a ragewa al’umma sauki.

Cutar covid 19 ta dakatar da komai a fadin kasar Inda a halin yanzu masu dauke da cutar a najeriya sun kai mutane 232 sannnan wanda suka warke sun kai mutum 33.

Related posts