Buhari Ya Umarci Ministoci Su Ci Gaba Da Aiki Har Ranar Jajiberin Mika Mulki


Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci ministocinsa su ci gaba da aiki har zuwa jajiberin ranar sauka daga mulki.

An yi ta hasashen shugaban zai rushe majalisar ministocin tasa a yau Laraba yayin zaman ƙarshe da ya jagoranta bayan shafe shekara takwas a kan mulki.

Sai dai shugaban ya umarce su da su ci gaba da aiki har zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu, kamar yadda Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu za a rantsar da shugaba mai jiran gado Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.

An gudanar da zaman ne a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mahalarta taron sun ƙunshi Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo da dukkanin ministoci 44 na gwamnati da kuma ƙananan ministoci.

An gabatar da jawabai na yadda al’amura suka kasance tsawon mulkin shugaban ƙasar da kuma jawaban ban-kwana.

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 ne Muhammadu Buhari ya hau kan mulki bayan doke tsohon shugaban ƙasa mai ci Goodluck Jonathan.

A lokacin da ya hau mulki, Buhari ya yi alƙawarin murƙushe rashin tsaro ta hanyar kawar da ƙungiyar Boko Haram, da yaƙi da rashawa da kuma yaƙi da talauci.

Labarai Makamanta