Buhari Ya Tsiyata Najeriya – Shugaban PDP

Zababben shugaban babbar jam’iyyar hamayya PDP ya ce yawan ciyo bashin da shugaban kasar Muhammadu Buhari yake yi ya sa kasar ta zama mabaraciya.

Sanata Iyorchia Ayu ya bayyana haka ne a wurin taron manema labaran da sabbin shugabannin jam’iyyar suka yi bayan taron karawa juna sani da suka yi a Abuja ranar Talata.

Ya ce a wajen taron da suka yi na kwana biyu sun gano cewa gwamnatin Buhari ta raba mutum miliyan 30 da ayyukansu, yana mai cewa gwamnatin ta gaza wajen samar da tsaro.

Haka matsalar tattalin arziki ta mayar da Najeriya cibiyar talauci a duniya, a cewar shugaban na PDP.

Ya ce PDP ta shirya tsaf don ceto Najeriya daga kanshin mutuwar da APC ta yi mata

Labarai Makamanta