Buhari Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 55

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon Shugaban Hukumar jin dadi da walwalar ‘yan gudun hijira Sanata Basheer Garba Lado murnar cika shekaru 55 da haihuwa, tare da addu’ar Allah kara wasu shekaru masu albarka.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasa ya yi tarayya da sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC, da iyalan Sanatan da sauran ‘yan uwa da abokanan arziki, wajen taya zakakurin Sanatan kuma gogaggen ɗan kasuwa wanda ya bada gagarumar gudummawa wajen ciyar da kasa gaba.

Buhari ya yi jinjina ta musamman ga tsohon Sanatan kuma tsohon Shugaban Hukumar jin dadi da walwalar ‘yan gudun hijira, bisa ga jajircewarshi wajen samar da shugabanci nagari a ƙasa.

Daga karshe Shugaban ƙasa Buhari ya yi addu’a kara samun lafiya da kwanciyar hankali ga Sanatan da addu’ar Allah ya yi wa iyalansa addu’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply