Buhari Ya Taya Ɗangote Murnar Cika Shekaru 64

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote murnar cika shekaru 64, inda ya bayyana wadannan shekarun a matsayin masu albarka sannan ya yi addu’ar ƙarin lafiya da kyakkyawan cigaba a gareshi.

A cikin wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, Shugaban ya bayyana Dangote, wanda ya cika shekaru 64 a ranar Asabar, a matsayin babban abokin tarayya kuma “Jarumin yakin Korona” wanda ya ci gaba da nuna cikakken imani da kasar Najeriya.

Buhari ya lura cewa duk da cewa annobar Korona ta sanya babbar damuwa ga kasashe da yawa, an dan rage matsalar ga ‘yan Najeriya da gwamnati, bisa kokarin Mutane irin su Aliko Ɗangote.

Shugaba Buhari ya danganta hakan da goyon baya da hadin kan ‘yan kasa kamar Dangote wanda ya ce suna matukar nuna jin kai da sadaukarwa ga dan adam ta hanyoyin su.

Ya kuma yaba mishi saboda bude fuka-fukansa da yake da burin karfafa matasa da kwararru da dama a Najeriya da ma sauran nahiyoyi ya kuma bukace shi da ya ci gaba da yin hakan.

Shugaban ya yi imanin wadannan kokari na Dangote za su shiga cikin tarihi kuma al’ummomi masu zuwa za su tuna da shi. Ya yi wa Dangote fatan karin shekaru masu yawa na rayuwa cikin koshin lafiya da yi wa kasarsa hidima da kuma bil’adama baki daya.

Labarai Makamanta