Buhari Ya Taka Gagarumar Rawa Wajen Samar Da Tsaro – Obasanjo

Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo yace masu sa ran Muhammadu Buhari zai iya yin abin da ya wuce wanda ya yi, su na bata lokacinsu, domin tabbas Buhari ya yi rawar gani.

Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wannan ne a wajen wani zama da Global Peace Foundation da Vision Africa suka shirya domin a tattauna batun tsaro a Abuja.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi jawabi a taron, inda ya yi kira ga shugabanni su daina siyasantar da sha’anin tsaro.

Anasu bangaren Samson Ayokunle, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, Audu Ogbeh da Bitrus Pogu sun tofa albarkacin bakinsu a madadin kungiyoyinsu na CAN, NEF, MBF da ACF.

Abin da Obasanjo ya fada a taron “Maganar gaskiya ita ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi iyakar abin da zai iya. Abin da zai iya kenan.” “Idan mu na sa ran ya yi abin da ya zarce wannan, kamar mu na dukan mataccen doki ne, kuma babu bukata.”

“Me kuma za mu yi bayan wannan? Ba za mu yi shiru, mu kwanta ba. Daga cikin abin da ya da kamata mu yi shine dagewa da addu’oi da sa ido kuma za mu cigaba.”

“Ya za mu shiryawa rayuwa bayan Buhari? Buhari ya yi bakin kokarinsa. Addu’a ta, Ubangiji ya sa ya gama wa’adinsa.” “Me za mu yi domin tanadi bayan tafiyar Buhari? Wannan nauyi da yake kan mu a halin yanzu, domin ya shafe mu duka.” Musamman wajen inganta rayuwar matasa wadanda sune makomar ƙasar anan gaba.

Labarai Makamanta