Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya Su Sa Amurkawan Da Guguwa Ta Hallaka A Addu’a

Rahotanni daga fadar Shugaban ƙasa dake babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Amurka da mutanen ƙasar kan mahaukaciyar guguwar da ta kashe sama da mutum 100 a jihohi shida.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya damu ƙwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci suka lalace.

Shugaban ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu’a ga waɗanda suka rasa ransu da kuma samun sauƙin wadanda suka jikkata.

Sama da mutum 100 ne suka rasu a guguwar wadda ta fi ɓarna a jihar Kentucky ta Amurka.

Labarai Makamanta