Buhari Ya Roki Kasashen Duniya Su Yafe Wa Najeriya Bashi

Rahoton dake shigo mana daga birnin New York na ƙasar Amurka na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya karo na 77 ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, ciki har da rashin iya bisa basussuka.

Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki domin a samu yafe basussukan ga matalautan ƙasashe.

“Najeriya na rokon takwarorinmu na duniya su taimaka mana. Lallai kalubalen da kasashe maso tasowa ke fuskanta yasa biyan basussuka zai musu wuya.”

“Hakazalika muna kira ga saukake basussukan ta hanyar tsawaita lokuta biya ga kasashe masu fuskantar matsalar kudi da kuma yafiya gaba daya ga kasashen da nasu matsalar tayi tsanani.”

Masu nazarin al’amurra a Najeriya na ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ƙaurin suna a matsayin Shugaban ƙasa guda ɗaya tilo a Najeriya da ya mayar da cin bashi tamkar kasuwanci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply