Buhari Ya Nuna Dattaku A Fatali Da Kudurin Zabe – Gwamnoni

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi abin a yaba kan ƙin sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓe da Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ita.

Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugaban ƙasar a fadarsa da ke Abuja.

Ya ce gwamnoni ba sa adawa da duk wani shiri na fitar da ƴan takara, sai dai ya kamata a yi abun da hankali zai ɗauka.

Gwamnan ya ce ”Bajintar da shugaban ƙasa ya yi ta amincewa da ra’ayin jama’a abun a yaba masa ne, domin abun da shi yake so shine a yi wa kowa adalci ko ma wane tsari za a bi”.

Labarai Makamanta