Buhari Ya Nesanta Kanshi Da Rikicin APC A Jihar Kano

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar Shugaban kasa ta yi fashin baki game da ikirarin da wasu yan siyasa a jihar Kano ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari na marawa wani tsagin shugabancin APC baya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya barranta maigidansa daga maganar marawa wani tsagi baya. Ya bayyana hakan a jawabin kar ta kwana da ya saki da daren Asabar, 25 ga Disamba, 2021.

Za ku tuna cewa APC ta rabe biyu a jihar Kano ana gab da gudanar zaben shugabannin jam’yyyar na jihar. Yayinda Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ke goyon bayan tsagi guda, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ke jagorantar dayan tsagin.

Labarai Makamanta