Buhari Ya Jajantawa Waɗanda Hatsarin Jirgin Ruwan Kebbi Ya Ci

Shugaban Ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu sanadiyyar hadarin jirgin ruwa da ya faru a yau akan hanyar jirgin ta zuwa garin Wara jihar Kebbi

A yau misalin karfe 10 na safe jirgin ruwa dauke da mutane maza da mata ya yi hadari akan hanyar sa ta zuwa wara jihar Kebbi, jirgin ya taso ne daga lokon minna jihar naija.

Shugaban kasa Buhari ya Jajanta masu tare da nuna alhini game da abun da ya faru, bayan yayi jinjina ga Waɗanda suka ci gaba da aikin fiddo gawarwakin.

Kawo yanzu dai an samu gawar mutum 5 a cikin mutane fiye da 160.

Labarai Makamanta