Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Ingila na bayyana cewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da sarkin Ingila Charles na uku a fadar Buckingham da ke birnin London.
Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Buhari da basaraken tun bayan hawan sa kan karagar mulki.
Bayanai na cewa ganawar ta bai wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari damar taya sarkin murnar hawa mulki.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan sada zumunta a shafukan intanet Bashir Ahmad ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na tuwita.
Kasar Birtaniya dai kamar yadda aka sani ita ta yi wa Najeriya mulkin mallaka tsawon shekaru har zuwa shekarar 1960 lokacin da Najeriya ta samu ‘yanci daga ƙasar.
Har ya zuwa wannan lokaci da muke ciki ƙasar ta Birtaniya na taka rawa akan harkokin siyasa da tsaron Najeriya.
You must log in to post a comment.