Buhari Ya Gaza Gaba Daya A Mulki – Kungiyar SERAP

Kungiyar nan mai rajin tabbatar da adalci a tsakanin yan kasa SERAP, ta gano wasu cin hanci da aka tafaka a ma’akatun ruwa, Lafiya da kuma ilimi, sannan ta roki shugaba Buhari da yai bincike akan ma’aikatun sabida alkawarin da yayi.

Kungiyar ta gabatar da wannan batun ne a lokacin da take zantawa da manema labarai kan alkwarurrukan da Shugaba Buhari ya kasa cika su a birnin tarayya Abuja.

“Gwamnatin Buhari ta gaza wajen yakar cin hanci da rashawa, girmamma doka da oda, samar da abubuwan more rayuwa da sauran abubuwa da ya kamata ace gwamnatin tayi ko ta dau alkawarin yi.”

Karuwar matalauta a Nijeriya na daga cikin abubuwan da Buhari ya sha alwashin magancewa amma abin takaici sai matalautan suka karu a Najeriya.

Wannan yake tabbatar da yadda shugaba Buharin ya gaza cika alkawarin da ya daukarwa yan Nijeria na fitar da su daga kangin talauci. Rashin aikin yi Haka zalika dai Ƙungiyar ta fitar da kiddigar yawan marasa aikin yi na karuwa da kaso 22 a kowacce shekara tunda daga hawansa mulki a shekarar 2015.

Kungiyar tace batun ace gwamnati na girmama umarnin kotu wannan batu ne wanda za’a iya cewa sai dai kallo domin akwai umarni da hukunce-hukunce da kotu ta yanke kuma take umartar ita gwamnatin ta aiwatar amma ina, abun ya zama kaman wasan kwaikwayo.

“Shi yasa muke kira ga yan takara na yanzu da suke kokarin neman kujarun da su san abin da zasu fada, kuma sun tabbatar da abinda zasu fadan wanda zasu iya aiwatar da shi.”

Labarai Makamanta