Buhari Ya Gaza Amma Munafunci A Yi Magana – Aisha Yesufu

Sananniyar matar nan ‘yar kishin kasa Aisha Yesufu ta yi magana a kan sace yara da ake ta yi a makarantun Arewacin Najeriya, ta ce abin sai dai ace “Innalilahi wa inna illaihi rajiun.”

A cewar Aisha Yesufu ba a taba ganin ‘yan bindiga su na zuwa su na dauke yara haka ba, amma gwamnati ta yi kunnen shegu, mutane kuma sun yi tsit.

Ta ce: “Wai ba za ayi magana ba saboda Buhari ne shugaban kasa. Amma idan da wani ne, alal misali wani da ba musulmi ba, da tuni an daina munafuncin nan, ana ta fito wa, ana magana.”

“Amma yanzu yawancin mutane an yi tsit, an zauna ana kallon ana dauke yara, Allah kadai ya san abin da aka yi masu” inji Yesufu.

‘Yar gwargwamayar ta ke cewa Ubangiji ne kadai ya san halin da yaran makarantun Arewa su ke ciki na dar-dar. Ta ce: “Wannan abin bai kamata, ba daidai ba ne.”

“Gwamnoni da shugaban kasa su ji tsoron Allah. Talakawan nan su ne su ka zabe su, su ka fito kwansu da kwarkwatarsu, su ka zauna a karkashin rana, su ka jefa maku kuri’a.”

Ta ce: “Mutane su na cikin wani hali, amma masu mulkin da aka zaba sun yi kunnen uwar-shegu.”

Duk da an yi sababbin zubin shugabannin hafsun sojoji, jagorar kungiyar BBOG ta ce ba a daina jin labarin ‘yan bindiga sun sace yara a makarantun yankin Arewa ba.

Yesufu ta yi tir da yadda shugaban kasa ya rika yabon tsofaffin hafsoshin sojoji, har ta kai an nada su jakadu a kasashen waje, ta ce don a cigaba da dama wa da su.

Bayan haka Yesufu ta ce ana neman a birne zargin da NSA, Babagana Monguno ya yi na cewa an salwantar da kudin makamai a karkashin tsofaffin hafsun sojoji.

Labarai Makamanta