Buhari Ya Dora Tubalin Ginin Sabuwar Hedikwatar ECOWAS A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas a Abuja babban birnin tarayya.

Shugabannin ƙasashen Guinea Bissau Umaro Embaló, da na Saliyo Julius Maada Bio, da Shugaban Ecowas Omar Alieu Touray, da Jakadan China a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka taya Buhari saka ɗambar ginin a ranar Lahadi.

Ana sa ran kammala sabuwar hedikwatsar a shekara ta 2025.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewa hamshaƙin ginin, wanda gwamnatin China ta samar da kuɗin ginawa, zai ƙarfafa zumunci a tsakanin ƙasashen Afirka.

Ginin zai kuma wakilci al’ummar Afirka ta Yamma mutum miliyan 380 sannan zai kasance matsuguni ga manyan cibiyoyin Ecowas uku, ciki har da ginin hukumar gudanarwar ƙungiyar da Kotun Ecowas, har ma da Majalisar Dokokin Ecowas.

A gefe guda kuma, shugabanin mambobin ƙungiyar na gudanar da taro karo na 62.

Labarai Makamanta