Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Kammala Hutu A Landan

Rahotanni daga fadar Shugaban Kasa dake birnin tarayya Abuja sun tabbatar da cewa mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya isa babbar tashar sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja daga birnin Landan bayan makwanni biyu inda yaje ganin Likita.

Rahotanni sun bayyana cewar Buhari ya isa Abuja ne da misalin karfe 5 na yammacin Alhamis, 15 ga Afrilu 2021, agogon Najeriya da Nijar.

Idan baku manta ba tun da safiyar ranar Alhamis ne muka kawo muku rahoto cewa komai ya kankama don dawowar shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kasa Buhari ya tafi birnin Landan na kasar Ingila tun a ranar 30 ga watan Maris da sunan zuwa duba lafiyarsa kamar yadda ya saba.

Labarai Makamanta