Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Halartar Taro A Murtaniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya koma gida bayan halartar taron zaman lafiya karo na uku da ƙungiyar zaman lafiya ta Afirka ta gudanar.

A lokacin halartar taron da aka gudanar a Mauritaniya, shugaba Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa ta kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sake ƙwato garuruwan da ke hannun mayaƙan Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

Haka kuma shugaba Buhari ya ɗora alhakin rashin daidaitar al’amuran tsaro a ƙasar da ma yankin tafkin Chadi kan rikice-rikicen da ake yi a ƙasashen Libya da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ma mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.

A wajen taron kuma Buhari ya karɓi lambar yabo ta ‘ƙarfafa zaman lafiya a ƙasashen Afirka” wadda ƙungiyar wanzar da zaman lafiya ta Afirka ta ba shi.

Labarai Makamanta