Buhari Ya Ci Amanar ‘Yan Najeriya – Sheikh Bello Yabo

Labarin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar a wajen wani sabon karatu da Sheikh Bello Yabo ya yi, ya yi Allah-wadai da gwamnatin Muhammadu Buhari, yace mulkinsa bai tsinana komai ba illa fitina da wahala ga Talaka.

Legit.ng Hausa ta samu faifen wannan karatu da Shehin Malamin ya gabatar, inda ya yi wa gwamnatin tarayya Allah ya isa, yace an zalunce al’umma. “Muhimmancin mulki shi ne ya kare rayuwa, dukiya da mutuncin talakawa, duk mulkin da ya kasa yin wannan, ai sai mu ce gara babu da shi.”

“Su wadannan (shugabanni), gara babu da su. Dama babu shugabanni sai mu san kara zube muke.” Buhari ya ci amana, idan kowa bai ci amana ba, shi Buhari ya san ya ci amana. Ba sai kowa ya fada masa ba, ya san ya ci amanar ‘Yan Najeriya.

Bello Yabo yace hukuncin kisa aka yanke masu saboda tsayar da suka yi sai Buhari ya samu mulki. Malamin yace yanzu an kashe wasu daga cikinsu.

Malamin yace mai girma shugaban kasa ya fi kowa sanin irin rawar da suka taka a dalilin shi, yace sun kuma yi haka ba domin abin Duniya ba, sai don gyara. Yabo yace ya yi gaba-da-gaba da mutuwa a baya, saboda kwadayin alkawarin da Buhari ya yi na cewa ba zai ci amana ko ya bari wasu su ci amanar al’umma ba.

“Babu wanda ya isa ya hana ni sukar gwamnati mai-ci domin duk Najeriya mutum biyu yake cirewa hula a game da son Buhari. “Daga matarsa, Aisha, sai Injiniya Buba Galadima. Bayan biyun nan, ban yarda akwai wanda ya fi ni yi wa Buhari wahala ba. Idan akwai, sai ya fito mu zauna.”

“Mu ba mu zuwa zanga-zanga, ba mu yin abin da ya saba doka. Amma da dokar Allah da ta nasara, babu wanda ta hana yin addu’a, Allah ka isar mana.”

Labarai Makamanta