Buhari Ya Bada Umarnin Tura Wa Matasa Kudade A Bankuna

Ma’aikatar kwadago da ayyukan yi ta Najeriya ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin fitar da makudan kudi domin soma biyan ‘yan Najeriya 774,000 da suka yi rijistar shirin SPW na tallafin korona.

Karamin ministan kwadago Festus Keyamo ne ya sanar da haka a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

Ya ce nan ba dadewa ba wadanda suka yi rijistar shirin za su fara jin kararrawa a asusunsu na banki mai nuna alamun tallafin ya shigo.

Kuma a cewarsa, za a yi amfani da lambar BVN ta banki domin kaucewa masu karba har sau biyu musamman wadanda suka yi rijista da suna biyu.

Sai dai ministan bai fadi lokacin da gwamnati za ta fara biyan wannan kudin ba.

A watan Janairu ne gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin na tallafi ga matasa 750,000 da ke zaman kashe wando yayin da rashin ayyukan yi tsakanin matasan ya yi kamari talauci kuwa ya yi katutu a cikin jama’a.

Labarai Makamanta

Leave a Reply