Buhari Ya Bada Umarnin Tura Ƙarin Soji 6000 Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin girke karin sojoji 6,000 a Jihar Zamfara domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Jihar da suka hada da hare-haren ‘yan bindiga da na masu garkuwa da mutane.

Gwamnan Jihar Bello Matawalle ne ya bayyana haka a jawabin da ya yi wa al’ummar jihar, bayan ziyarar da ya kai Abuja inda ya gana da shugaban kasar da kuma masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaron.

Matawalle yace wadannan sojojin 6,000 kari ne kan wadanda ake da su yanzu haka, ganin yadda matsalolin tsaron ke cigaba da ta’azzara, kuma zasu isa jihar nan bada dadewa ba.

Gwamnan yace shugaba Buhari ya amince da lokacin da aka diba domin shirin afuwar da suka gabatarwa yan bindigan domin aje makaman su, ganin nasarorin da aka samu.

Matawalle yace duk da wadannan nasarori akwai wadanda suka ki aje makamai, kana kuma akwai masu yiwa shirin nasu zagon kasa a ciki da wajen jihar. Gwamnan ya bayyana daukar wasu matakai da ake ganin zasu taimaka wajen dakile aikata laifuffukan da suka hada da hana tafiye tafiye ga Sarakuna da shugabannin kananan hukumomi domin sanya ido kan bakin dake zuwa yankunan su. Gwamnatin jihar ta kuma haramta daukar fiye da mutuum guda a babur da kuma hana tafiyar tawagar Babura yankunan jihar, inda aka bukaci jami’an tsaro da su kama wadanda suka sabawa umurnin.

A karshe Gwamnan ya jaddada haramta ayyukan Yan Sakai a fadin jihar, yayin da yake cewa duk wanda aka gani dauke da bindiga za’a hukunta shi.

Labarai Makamanta