Buhari Ya Bada Umarnin Dakatar Da Rantsar Da Shugabannin NNPC

Labarin dake shigo mana daga fadar Shugaban Kasa na bayyana cewar Shugaba Buhari, ya bada umarnin ɗage shirin rantsar da sabbin shugabannin kamfanin man fetur na ƙasa NNPC har sai abin da hali ya yi.

An ruwaito shirin rantsar da su da aka tsara gudanar wa ranar Laraba, an ɗage shi har zuwa wani lokaci nan gaba.

Sai dai babu wani cikakken bayani da gwamnatin tarayya ta bayyana kan dalilin ɗage rantsar da mutanen.

A wata sanarwa da da sakataren gwamnatin tarayya,Boss Mustapha, ya fitar, ya bayyana cewa za’a sanar da sabuwar rana idan lokacin ya yi.

3- Da Yiwuwar Farashin Mai Ya Kai 340 A Shekarar Baɗi

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari ya ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya kai N340 a shekarar 2022.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya na watan Nuwamba a Abuja ranar Talata.

Ya ce babu makawa za a cire tallafin mai a cikin shekarar mai zuwa, kamar yadda doka ta tanada.

“Babu wata doka da za ta tanadi ci gaba da biyan tallafin mai, amma na tabbatar za ku yaba wa tsare-tsaren da gwamnati za ta bullo da su don jin dadin jama’a, da nufin ganin talakawa ba su sha wahala ba,” inji shi.

Labarai Makamanta