Buhari Ya Bada Kwangiloli 878 Cikin Shekaru Shida – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar daga kafuwar gwamnatin Muhammadu Buhari a watan Mayun 2015 a Najeriya, majalisar zartarwa ta kasa watau FEC ta bada kwangiloli har 878.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana haka a wajen taron bitar da aka shirya wa Ministoci a farkon makon nan, a birnin tarayya Abuja.

Haka zalika majalisar FEC ta amince da tsare-tsare 319 da bayanai da tattaunawa 206 tsakanin watan Nuwamban shekarar 2015 zuwa watan Agustan 2021.

Rahoton yake cewa Boss Mustapha bai yi karin bayani kan kwangiloli da tsare-tsaren da gwamnatin APC ta bada ko ta kawo a wadannan shekaru ba.

Amma mafi yawan kwangilolin da majalisarta FEC ta bada na samar da abubuwan more rayuwa ne da nufin farfado da tattalin arziki da kawo cigaban kasa. Kwangiloli 878 a watanni 71 “Adadin kwangiloli, tsare-tsare da bayanan da majalisar zartarwa na tarayya ta bada tsakanin Nuwamban 2015 da Agustan 2021 sun kai 1, 403.” “Daga ciki akwai kwangiloli 878, tsare-tsare 319, da bayanai da tattaunawa 206.”

Bayan gwamnatin Buhari ta zarce a mulki Sakataren gwamnatin yace daga ranar 29 ga watan Mayu, 2019 zuwa 31 ga watan Agusta, 2021, majalisar FEC tayi zama sau 52, kuma ta amince da takardu 579.

Daga cikin takardun da aka amince da su akwai na kwangila 381, tsare-tsare 110 da bayanai 52.

A cewar Boss Mustapha, wadannan alkaluma sun nuna kokarin shugaba Muhammadu Buhari na ganin an share wa al’ummar Najeriya kafin Mayun shekarar 2023.

Labarai Makamanta