Buhari Ya Amince Da Samar Da Kwalejojin Ilimi A Jihohi Shida

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude sabbin kwalejin horon malamai guda shidda; daya a kowanne bangare 6 na kasa.

Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Za a samar da sabbin Kwalejojin ne a jihohin Bauchi, Benuwe, Ebonyi, Osun, Sokoto da Edo.

A wata takarda kuma da ta fito mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar ilimi, Sunny Echono, ya ce an tsayar da ranar 11 ga watan Mayu domin ziyartar wuraren da za a bude kwalejojin a jihohin.

Related posts