Buhari Ya Amince Da Sabbin Matakan Tsaro A Kudancin Najeriya

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabbin matakan tsaro ga yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu na kasar, cikin gaggawa.

Wannan na daya daga cikin sakamakon jerin tarurrukan tsaro da aka gudanar a cikin kwanaki 11 da suka gabata kuma aka kammala a ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Mukaddashin Sufeto-janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Gwamnatin bayan taron, amma, ya ki ba da cikakken bayani sosai.

Shugaban ya kuma amince da wata takarda da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) ya gabatar, kan batun shan muggan kwayoyi, wadanda ya ce suna taimakawa Rashin tsaro, amma kuma bai yi karin bayani ba.

Labarai Makamanta