Buhari Ya Amince Da Kafa Hukumar Hana Yaɗuwar Makamai

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai a kasar.

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, ya ambato mai magana da yawun ofishin mai ba Buhari shawara kan sha’anin tsaro yana cewa hukumar za ta kasance a ofishin nasu.

Hukumar za ta maye gurbin kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar kananan makamai, in ji sanarwar.

Kafa hukumar “na cikin matakan inganta tsaron Najeriya domin magance barazanar tsaro da kuma karfafa shirin da kasashen yankin ke yi wajen takaitawa da magance matsalar yaduwar kananan makamai,” a cewar sanarwar.

A baya dai Shugaba Buhari ya sha kokawa kan karakainar kananan makamai da ma manya cikin kasar, lamarin da ya ta’allaka da yakin da aka yi a kasar Libya.

Hukumomi sun bayyana cewa akwai dubban kananan makamai a hannun ‘yan kasar, abin da ke ta’azzara hare-hare da kuma yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya.

Labarai Makamanta