Buhari Ya Amince Da Kafa Gagarumin Kamfani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da samar da wani kamfanin hadin guiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu mai suna Infra-Co, tare da fara wa da jarin Naira Tiriliyan daya.

Ana sa ran karfin jarin kamfanin zai bunkasa zuwa Naira Tiriliyan 15.
Kamfanin wanda shi ne irinsa na farko a Nahiyar Afirka, zai maida hankala ne wajen ci gaban ayyukan more rayuwa a kasar.

Kamfanin wanda shugaban Buhari ya bukaci mataimakinsa ya jagoranci kafa shi, Babban Bankin Nijeriya tare da Majalisar Bunkasa Tattalin Arzikin kasar suka kirkiro shi.

Kamfanin wanda CBN zai jagoranta, zai kunshi ma’aikatar zuba jari, shugaban hukumar kudi na Afirka, da wakilan kungiyar gwamnonin Nijeriya da kuma Ma’aikatar Kudi da Kasafi ta Nijeriya.

Labarai Makamanta