Buhari Na Neman Karbo Bashin Fiye Da Naira Triliyan Biyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na son ya sake ranto dala biliyan 6.1 daga ƙungiyoyin ƙasar waje domin cike giɓin kasafin kuɗi na 2021.

Jumillar kuɗin a naira sun kai tiriliyan N2.343 – kan canjin N379 a kowace dala.

Cikin wata wasiƙa da ya aike wa majalisun tarayyar ƙasar a ranar Talata, Buhari ya nemi amincewarsu domin karɓo wani sabon bashin.

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Idris Wase, shi ne ya karanta wasiƙar a zauren majalisar, yayin da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya karanta a tasu majalisar.

Kasafin kuɗin na 2021 ya nuna cewa za a samu giɓin naira tiriliyan biyar daga cikin jumillar tiriliyan 13.6.

Labarai Makamanta