Buhari Na Dab Da Kashe Najeriya Da Bashi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike wasika ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, inda ya bukaci majalisar kada ta sake baiwa Buhari daman karban basussukan da ba zasu haifar da ‘da mai ido ba.

A wasika mai ranar watan 25 ga Agusta, Atiku ya yi kira da yan majalisar dokokin tarayya su tsagaita ba Buhari daman karban bashin da ba zai kawo kudi ba.Ya ce Najeriya za ta iya shiga mawuyacin hali idan aka cigaba da karban basussuka saboda wadanda aka karba ba abubuwan kwarai akayi da su ba.

A cewar ofishin kula da basussukan Najeriya DMO, bashin da ake bin Najeriya kawo Maris 2020 ya kai $79.3 billion.Ko a watan Yuni, Ahmad Lawan ya sanar da cewa mambobin majalisan dokokin tarayya sun amince Buhari ya karbi bashin $28 billion.

A wasikar Atiku yace: “A ranar 29 ga Mayu, 2015, bashin da Najeriya taci ya kai Tiriliyan 12. Amma yanzu Agusta 2020, bashin ya ninku sau uku zuwa N28.63 trillion.”

“Abin damuwa a nan shine wadannan basussuka basu da muhimmanci kuma ba’a bukatarsu. Binciken da akayi kan abubuwan da akayi da kudaden ya nuna cewa ba wasu ayyukan kirki masu kawo kudi akayi da su ba.”
“Saboda haka, a matsayinku na masu duba abubuwan da sauran bangarorin gwamnati ke yi, ina mai bukatan daga yanzu, kada majalisar dokokin tarayya ta kara bada daman karban sabon bashin da za’a yi amfani wajen ayyuka maras kawo kudi ko marasa amfani.”

Labarai Makamanta