Buhari Estate Mallakar ‘Yan Sanda Ne Ba ‘Yan Bindiga Ba – ‘Yan Sanda

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun mamaye wani rukunin gidaje mai suna Buhari Estate da ta mallaka a yankin Badagry na Jihar Legas.

Cikin sanawar da fitar a ranar Asabar, rundunar ta ce wani mutum ne “da ya yi kama da mai ilimi wanda ya kamata a ce ya san haɗarin yaɗa labaran ƙarya yake yaɗa bayanai da zimmar tayar da fitina” a wani bidiyo, yana iƙirarin cewa ‘yan bindiga ne suka mamaye rukunin gidajen.

Sanarwar ta ce rukunin gidajen mallakin rundunar ne kuma jami’an ‘yan sanda ne da iyalansu suka mallake su ta hanyar wani shirinta.

“Rundunar ‘yan sanda na shawartar mutane kan muhimmancin tantance abu kafin yaɗa shi don kauce wa tashin hankali, musamman idan aka yi la’akari da mabambantan ƙabilun da ke cikin ƙasa Najeriya.

Labarai Makamanta