Buhari Bai Da Ƙwarewar Mulki – BBC Faruƙ

Dr Faruk BB Faruk mai sharhi akan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa ”rashin fasahar iya gudanar da mulki na janar Buhari na daya daga cikin dalilan da yasa kasar ke cikin shakakin kalubalen tsaro da tabarbarewar tattalin arziki.

Dr Faruk ya bayyana hakan ne a cikin shirin Babbar magana da ake gabatarwa a gidan talbijin da radio na liberty dake babban birnin tarayya abuja.

Yace ko a maganar karin kudin mai da akayi ban yarda cewar kuskure akayi ba, kawai an bayyana matakin ne aga yadda ‘yan najeriya zasu karbi lamarin kamin a tabbatar da matakin a hukumance. Domin a cewar Dr Faruk hukumar kayyade farashin albarkatun man fetur ita kadai bata isa ta kara kudin mai ba tare da sahalewar matatar mai da gwamnatin tarayya ba. Dr Faruk ya zargi kungiyar kwadago da cewar har da su a wasu lokutan ake tsara yadda za a kara azabtar da ‘yan najeriya da karin farashin man fetur wanda karin bai karewa akan kowa sai talaka.

Yace inda gwamnati nada tunani da fasahar habaka tattalin arziki, da man da muke saidawa muke anfani da kudaden, inda ace mune muke sarrafa man fetur din da matatun mu a cikin kasar mu, muna sarrafa sauran abubuwan da ake cirowa a cikin danyen man bawai man fetur kadai ba da ake siyan sa akan farashin duniya, da ansamu cigaba sosai. Amman a halin da muke ciki a yanzu karamar kasa kamar Nijar wanda bata kaimu a komai ba wai ita har tana iya tace danyen mai har ta kuma saidawa manyan kasashe kamar najeriya, Wannan kadai ya ishemu zama babban kalubale.

Shima Saminu Sani wanda ma’aikacin kafar tashar yanci ne, ya bayyana cewa duk da kasar nijar da kudaden bashi daga kasar chana suka gina nasu matatan man fetur din, me zai hana kasar mu najeriya itama tai anfani da makudan kudaden da ta ke ciyowa basukan su a kasashen duniya wurin gina sababbin matatun man fetur ko a gyara wanda muke dasu su ta yadda zasu kasance ingantattu?

Banda man fetur muna da arzikin kasa sosai a fadin kasar mu najeriya kuma duk kasashen duniya babu kasar da ‘yan kasar ta ke shan wahalar mai kamar najeriya kuma rashin samun shuwagabanni masu nagarta ne ya kara jefa mu cikin wahalhalu kala kala.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin gina matatun mai sababbi dal amman har yanzu babu abinda za kaga anyi da zai nuna maka an dauko hanyar gina su. Kuma wai yanzu saboda koma bayan da kasar nan ta fada har nijar ake zuwa domin a siyo mai.

Labarai Makamanta