Buhari Bai Cancanci Shugabancin Kasa Ba – PDP

Jamiyyar PDP tace kwatakwata shugaban kasa Muhammad Buhari bai dace da cigaba da zama a matsayin shugaban rundunar tsaron kasar nan ba duba da yanda ya gaza wajen kawar da yan bindiga da yan ta’addar da suka mamaye kasar nan.

PDP tace kalaman kwanan nan da tsohon shugaban hafasan sojojin kasar nan , Lt. Janaral Tukur Burutai ya furta, inda yace indai aka cigaba da yanda ake yakar wadannan yan ta’addar akan hanyar da akebi yanzu zamu iya shafe shekara 20 bamu kawo karshen yan ta’addar ba, wannan ya tabbatar da gazawar Buhari a matsayin babban hafsan tsaron kasar nan.

Jamiyyar tace abun bakincikine a ce yanzu muna matsayin da wasu daga cikin jami’an gwabnati da wasu yan Najeriya suke rokon da a tattauna da yan ta’addar, wannan ta kara fitowa fili da gazawar gwabnatin Buhari da kuma yanda ya sallamar da kasar nan ga yan ta’adda, yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane .

Dadin dawa, kalaman da ministan tsaron kasar nan , Janaral . Bashir Magashi yayi , inda yake kiran yan Najeriya da basu da makami su tunkari yan ta’addar dake dauke da mugan makamai , ya kara tabbatar da gazawar Buhari a matsayin babban hafsan tsaron kasar nan, bazai iya sauke nauyin da yake karkashin ofis dinsaba .

Abun sha’awar shine daya daga cikin mukarabban gwabnatin sa ya tabbatar shugaban kasa bashi da gogewa da kwarewar da zai kare rayukan yan kasar nan.

Abun bakinciki Fadar shugaban kasa Buhari da kanta ta zargi wasu da yan ta’addar sukayiwa kisan gilla da laifinsune ,lokacin da aka kashe manoma 43 a Jihar Borno , maimakon su gaggauta daukar mataki .

Irin wadannan cin zarafun da akewa yan Najeriya a wannan gwabnatin ta Buhari wajen yaki da yan ta’adda, ya jawo , kowa yana tuna lokacin mulkin PDP yadda aka dunga fatattakar wadannan yan ta’addar .

Yan Najeriya bazasu manta abun kunyar daya faruba yayinda shugaban kasar Chadi Idris Derby ya jagoranci fatattakar yan ta’addar wadda ya kwato wasu garuruwan dake Najeriya kai harma da sojojin dake hannunsu , shi kuma shugaban kasar mu yana cigaba da shoshalewarsa a fadar sa Villa .

Tabbas , duk babban hafsan da bazai iya jagorantar yaki ba , kamar yadda shugaban kasa Muhammad Buhari yayi alkawari ba , babu Wanda ya kamata ya zarga sai kansa akan gazawarsa , kuma ya tabbatar da gazawar sa.

Tabbas , Kasarmu bazata cigaba da zama cikin malalar jini kullum ba , garkuwa da mutane da kuma hare haren yan bindiga ba.

Jamiyyarmu tana kira ga shugaban kasa Buhari daya gaggauta kawo karshen wasan da ake da harkar tsaron rayukan yan kasar nan a mulkinsa .

Ya zama dole shugaban kasa ya tashi tsaye wajen sauke nauyin da yake kansa a matsayinsa na babban hafsan tsaron kasar nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply