Buhari Bai Ɗauko Hanyar Magance Matsalar Tsaro A Arewa Ba – Shugaban Matasa

An bayyana cewar ko kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari bai dauko hanyar magance matsalar tsaro wadda ta daɗe tana addabar yankin Arewa ba, illa sake dagula al’amurra da ya yi.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa, a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

Shugaban matasan ya ƙara da cewa abin takaici ne da yin tir ‘yan Ta’adda na kisan jama’a babu ji babu gani a Jihohin Arewa maso yamma, amma Shugaban ƙasa ya fito yana maganar wai ya bada wa’adin watanni biyu ‘yan Bindiga su miƙa wuya ko a gama dasu, wanda wannan kalami kuskure ne dake nuna tamkar an lamunce wa ‘yan Bindiga su cigaba da kisan jama’a kenan har na tsawon watanni biyu.

Kamal Funtuwa ya bayyana cewar tun asali ba’a dauko hanyar da ta dace bane akan batun magance matsalar tsaron wanda hakan ne ya sanya abubuwa ke cigaba da samun tawaya, kuma zasu cigaba da tafiya a haka muddin ba’a gyara ba.

Shugaban Matasan ya bada misali da matsayin da Jihohin Yarbawa suka dauka na samar da kungiyar Amotekun mai yaƙi da ‘yan Ta’adda, da yake sun sa niyya da kishin yankin su abubuwa basu taɓarɓare musu ba, amma a lokacin da matasa a yankin Arewa suka yi niyyar samar da kungiyar tsaro ta Shege Ka Fasa, nan take ake yaƙe su a rusa niyyar tasu saboda tsagwaron ƙin gaskiya.

Kamal Nasiha Funtuwa ya ƙara da cewar inganta rayuwar jami’an tsaron ya kamata Buhari ya yi ta fuskar wadata su da makamai na zamani wanda za su fuskanci ‘yan Ta’adda dasu ba iƙirari da baki ba.

“A kwanan nan Sojoji 115 suka ajiye aiki saboda yadda abubuwa suka dagule a rundunar, ashe abin da ya kamata shine Shugaban ƙasa ya duba daga ina matsalar take ya magance ta, ba yawaita surutai ba”.

Labarai Makamanta