Buga Labarin Karya: Kwamishinan Tsaro Ya Maka Dan Jarida Kotu

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kwamishinan Tsaron jihar Samuel Aruwan, ya zargi wata kafar yada labarai ta yanar gizo da kirkirar karya da kuma tunzura jama’a a kansa.

A ranar Talata Aruwan ya ce ya kai kara wurin hukumar tsaro ranar Lahadi saboda buga wannan labarin ƙarya da ya ke zargin jaridar ta yi masa.

A taron da ya yi da manema labarai ranar Talata Aruwan ya yi bayanin kan matakin da ya dauka kan wannan labari da wani ɗan jarida mai suna Luka Binniyat ya rubuta a kansa.

Aruwan ya ce “A ranar 29 ga Oktoba, 2021 hankalina ya karkata ga labarin da Binniyat ya rubuta a yanar gizo cewa Sanata Danjuma Laah na yankin Kudancin Kaduna ya bayyana masa cewa ana amfani da ni wajen boye kisan kiyashin da aka yi wa Kiristoci a Kudancin Kaduna.

“Kafin na tambayi sahihancin labarin hankalina ya yi matuƙar tashi kan illar da irin wannan labari zai haifar ga zaman lafiya da tsaro a jihar musamman saboda addini da kabilanci da ya saka a ciki da kuma irin zaman da ake yi a jihar Kaduna.

“Wannan labari da Binniyat ya rubuta ya jefa ni da iyalina cikin mummunan haɗari.

“Dole ne ku san abubuwan da ke faruwa a jihar Kaduna, a cikin shekaru 40 da suka gabata, an yi asarar dubban rayuka da dukiyoyi, sannan har yanzu gwamnati na kokarin kwantar da gargaɗin mutane su kiyaye daga fadin mugayen kalamai da za su iya tada zaune tsaye.

Idan ba a manta ba ‘yan bindiga sun kashe mutane a Zangon Aya da ke karamar hukumar Igabi, bayan nuna musu wariya da aka yi sannan da kisan wasu mutanen da aka yi a Doka bayan an yi musu lakabi da ‘masu cin amana’ saboda sun nuna kiyayyar su da yadda ake karkatar da ra’ayoyin mutane ta hanyar jinginata da kabilanci da addini.”

Aruwan ya ce bayan ƙarar da ya kai ga hukumomin tsaro domin gudanar da cikakken bincike, ya kuma sanar da kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a matakin kasa da jihar Kaduna.

Bayan haka Aruwan ya nemi ƙarin bayani da samun tabbacin ko da gaske ne akwai lokaci da Sanata Danjuma Laah ya furta kalaman da Binniyat ya zargi Aruwan da su.

Aruwan ya ce Sanatan da aka ambato a jaridar La’ah, ya musanta yin hira da Binniyat.

A cikin amsar da Laah ya bada ta kakakin sa, ya ce bai taba zama da wani ɗan jarida mai suna Binniyat ya yi hira da shi ba game da abubuwan da aka ce ya wallafa.

” Ban yi haka da wani ba. Aruwan kamar ƙanina ne saboda haka kada wani ya cukuikuyani cikin abinda ban sani ba.” In ji Laah.

Ko da aka nemi ji daga bakin Binniyat, ya aika sakon cewa ba zai iya magana ba yanzu domin yana tsare ne wajen ƴan sanda.

Labarai Makamanta