Budaddiyar Wasika Ga Malaman Jihar Zamfara

Daga Ibrahim Madugu Gusau

Malamai Masu Girma, da fatan wannan saƙo ya same ku cikin ƙoshin lafiya.

Na zaɓi in isar da wannan saƙo ta wannan kafa domin ƙara jawo hankalin ku akan kalaman da sabon mataimakin gwamnan Zamfara, Sen. Hassan Nasiha ya furta a gaban ku ranar 10 ga watan Maris, 2022 inda yake cewa “a shekarar 2011 IMANI ne yasa suka faɗi zaɓe” amma yanzu “babu wanda ya isa ya karbi mulki a hannun su!” Hakan ya ja hankali na har nayi rubutu mai taken: “TSOKANAR ALLAH (SWA) DA CIN FUSKAR MALAMAN ADDINI DA ALH. HASSAN NASIHA YAYI BABBAN ABUN KYAMA NE”.

Hakika na ɗauki wannan batu da girman gaske duba da munin kalaman mataimakin gwamnan da kuma fitinar da waɗannan kalaman ke iya haddasawa a wannan jaha tamu mai fama da dimbin matsaloli. Haka zalika, kalaman suna ƙona zuciya duba da cewa an furta su ne a gaban malamai (Magada Annabawa) kamar yadda nayi bayani a wancan rubutun da ya gabata.

Ko shakka babu nayi tsammanin inji majalisar malamai sun fito sunyi Allah wadai da wuɗannan kalaman na mataimakin gwamna da kuma kira gare shi da ya janye waɗannan kalamai kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya umurce mu da idan mun ga wani abin ƙyama to mu kawar dashi da hannun mu ko da harshen mu ko kuma mu ƙyamace shi a zuciyar mu (wanda yin hakan shi ne mafi rauni daga cikin imani).

Akwai alamar tambaya ganin cewa bayan malaman sun kama bakunan su sun yi shiru akan wannan ƙazamin al’amari da ya kamata suyi Allah wadai dashi, sai gashi kuma ranar 14 ga watan Maris (wato kwana huɗu bayan ziyarar), gwamnatin Zamfara ta umurci hukumar ZAPA da ta baiwa dukkanin ‘yan majalisar kimanin su 33 Keke Napep, ko wannen su. Hakan ya ƙara saka man shakku cewa mai yiyuwa anyi hakan ne domin a toshe ma malaman baki akan wuɗannan kalamai na mataimakin gwamna da ma duk wani karan tsaye da za’ayi wa addinin Musulunci domin a ci zaɓe!

Wani abin da ya ƙara jan hankali na shi ne yadda aka ware wani malami kwara ɗaya tilo mai suna Malam Yusuf Sambo aka hana masa kyautar da aka ma sauran malaman ‘yan uwansa duk da shima yana cikin majalisar. Bincike ya nuna cewa an ware malamin ne har sai an tabbatar da inda ya dosa (a siyasance) saboda ana zargin yayi wani wa’azi inda ya soki kyautar maƙodan kuɗin da gwamnan Zamfara, Hon Bello Matawalle ya ba ‘yan kokowa a ƙasar Nijar a shekarar da ta gabata.

Ya kamata malamai ku ji tsoron Allah kada ku sayar da mutuncin addini saboda ɗan abin da gwamnati ke baku wanda nayi imani suna yi ne domin toshe maku baki da ɓata maku suna. Ku sani ilimin da Allah ya baku amana ce kuma za’a tambaye ku akan wannan amana. Kuma ku sani cewa kuna da gudunmawa da ya kamata ku bayar domin isar da saƙon Allah (SWA) da kuma tarbiyyar al’umma ba tare da la’akari da girman wanda yayi ba daidai ba sai don la’akari da girman Allah (SWA) da kuma kare martabar addinin Musulunci.

Hakika rashin fitowa ku nesanta kan ku daga waɗannan kalaman tare da yin Allah wadai da su, da kuma ƙoƙarin rufe maku baki da dukiyar al’umma a lokacin da jahar Zamfara ke fama da dubban yan gudun hijira ba karamar illa zai haifar ba a zukatan al’umma.

Daga ƙarshe ina ƙara kira gare ku da ku nisanci duk wani abu da zai zubar maku da ƙima ya kuma zubar da darajar addini. Ina kuma rokon Allah Ya albarkaci mutanen Zamfara da shuwagabanni masu imani ba masu ganin imani barazana ba ne ga muradun su na duniya. Amin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply