Borno: Zulum Ya Yi Wa ‘Yan Gudun Hijira Sha Tara Ta Arziki

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da tsabar kudi har sama da rabin biliyan daya.

‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.

A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.

Sansanin na Bakassi, wanda gini ne da gwamnati ba ta kammala ginawa ba a kan titin Maduguri zuwa Damboa, cike ya ke da ‘yan gudun hijira da suka kai shekaru 7 a cikin, waɗanda bala’in Boko Haram ya tarwatsa.

Akwai ‘yan Monguno, Gwoza, Guzamala da karamar hukumar Marte. Mata da dama suna ta haihuwar yara kusan duk shekara.

Zulum ya nuna rashin amincewarsa da yadda sansanin ya zama wuri na dindindin da wasu suke yada zango ba tare da dagewa wurin taimakon kansu da kansu ba.

A cikin N500,000,000 din da gwamnan ya bayar yayin ziyarar ta sa, kowanne mace da namiji wadanda yawanci zawarawa ne sun samu N100,000, buhunan shinkafa 2 masu 25kg, katan na taliya da lita 5 na man girki.

Matan aure kuma sun samu N50,000 baya ga N100,000 da aka ba mazajensu tare da tarin kayan abincin.

Labarai Makamanta