Borno: Zulum Ya Yi Wa Kwamishinoni Garambawul

Rahotanni daga Jihar Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum, ya aiwatar da kwarya-kwaryar garambawul a cikin majalisarsa tare da sauya kwamishinoni uku, jim kaɗan bayan dawowarsa daga aikin Umrah.

Shawarwarin na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata daga mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, Danjuma Ali.

Ali ya ce an mayar da Kwamishiniyar Albarkatun Dabbobi da Bunkasa Kiwon Kifi, Juliana Bitrus zuwa Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Dan Adam, Kwamishinan Muhalli, Alhaji Lawan Walama, yanzu shi ne zai kula da Ma’aikatar Albarkatun Dabbobi da Bunkasa Kiwon Kifi.

Ali ya kuma bayyana cewa Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Alhaji Kaka-Shehu Lawan yana da karin aikin kula da Ma’aikatar Muhalli.

A wani labarin kuma, Zulum ya amince da sake kafa hukumar kula da cigaban kiwon lafiya matakin farko ta Borno tare da nada Ahmed Tijani a matsayin Shugaba. Ali ya ce Zulum ya kuma amince da nadin Dakta Joseph Jatau a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Asibitocin Borno nan take da kuma Abubakar Suleiman a matsayin Mukaddashin Janar Manaja na Hukumar Kare Muhalli ta Borno.

A cewar Ali, gwamnan kamar yadda sashi na 9 karamin sashi na 1 na dokar hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta shekarar 2013, ya amince da nadin Dr Abba Goni a matsayin Darakta na Hukumar Bunkasa Kiwon Lafiya a matakin farko ta jihar. Wadannan sauye-sauye sun biyo bayan bankado wata badakalar ma’aikatan bogi da gwamnatin jihar ta Borno ta bankado ne.

Labarai Makamanta