Borno: Zulum Ya Yi Nasarar Gano ‘Yan Gudun Hijira Na Bogi

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa wani sansanin ‘ƴan gudun hijira dake Maiduguri shigar ba-zata inda ya gano ɗaruruwan ‘ƴan gudun hijirar na bogi danƙare cikin sansanin.

Sanarwar da gwamnatin Jihar Borno ta aike wa Ƙungiyar ‘yan Jaridu ta ce daga cikin ‘ƴan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami’an agaji, 650 daga cikinsu na bogi ne.

Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS dake birnin Maiduguri inda ake kula da mutanen ƙaramar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya raba da gidajensu.

“Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin ‘ƴan gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ‘ƴan gudun hijirar,” in ji sanarwar.

Sannan ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin gano masu ƙaryar cewa ‘ƴan gudun hijira ne da ke shafe kwanaki a sansanin suna karɓar abincin da aka tanadar wa ‘ƴan gudun hijira, kuma idan dare ya yi su tafi gidajensu.

Jama’a na cigaba da yabawa gami da jinjina ga gwamnan bisa namijin ƙoƙarin da yake wajen inganta al’amura da rayuwar jama’ar Jihar gaba daya.

Labarai Makamanta