Borno: Zulum Ya Raba Wa Jami’an Tsaro Motocin Aiki

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba wa jami’an tsaro motoci 18 domin gudanar da sintiri da zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukan tsaro a fadin jihar.

A wani mataki na karfafa gwiwa Zulum ya bayar da motocin ne ga sojoji da jami’an JTF ‘yan sa kai da ke sintiri a kan babbar hanyar Maiduguri- Dikwa- Gamboru.

Ya bayar da motocin ne ga kwamandan rundunar Hadin Kai Manjo Janar Christopher Musa, yayin da ya sanya azamar sake bude babban hanyar kasuwanci da take hada Muna da Maiduguri a ranar Juma’a.

Bayan bude hanyar ya kuma karasa garin Dikwa domin tabbatar da matafiya na zirga-zirga lafiya zuwa Gamboru, kan iyakar Ngala.

Labarai Makamanta