Borno: Zulum Ya Haramta Raba Abinci Ga ‘Yan Gudun Hijira

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya haramta raba abinci ga dubban ƴan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Manufar matakin shi ne domin taimaka masu yin dogaro da kai. Sai dai wasu na ganin matakin zai ƙara haifar da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin Borno ta daɗe tana son rufe sansanonin ƴan gudun hijira domin mayar da su garuruwansu.

Gwamnan yanzu ya haramta wa ƙungiyoyin agaji raba abinci ga waɗanda suka samu matsuguni domin su yi dogaro da kansu.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya na fuskantar barazanar ƙarancin abinci saboda har yanzu yin noma na da hatsari. Wasu ƙungiyoyi agaji sun ce taimakon har yanzu yana da amfani.

Labarai Makamanta