Borno: Zulum Ne Ya Sa Na Mika Wuya – Kwamandan Boko Haram

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar wani kwamandan Boko Haram da ya mika wuya mai suna Mallam Adamu Rugurugu, ya bayyana dalilin da yasa ya ajiye makaman yakinsa. Rugurugu ya bayyana cewa ya yanke shawarar fitowa daga jeji tare da mayakansa da dama saboda roko da shiga lamarin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi.

Da yake magana a sansanin da aka ajiye fiye da yan ta’adda 14,000 da suka mika wuya tare da iyalinsu a Maiduguri, Rugurugu ya ce ya samu sunansa ne daga ayyukansa a filin daga yayin da suke arangama da dakarun gwamnati.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa daga baya ya gano cewa abun da yake yi ba daidai bane kuma da gaske gwamnati take zata karbe su. Ya ce a dalilin haka ne ya yanke shawarar taimakawa wajen lallashin mayaka da dama kan su fito daga jeji sannan su mika wuya.

“Eh ina daga cikin kwamandojin. Na samu sunan Rugurugu wanda ke nufin babu tausayi daga filin daga. A filin daga ina da matukar hatsari saboda ina lalata duk abun da ya zo hanyata. Bani da tsoro. Wadannan makin da kuke gani a jikina ya kasancewa saboda rashin tsorona.

Gwamna ya ji labarina sannan ya san cewa idan aka lallaba ni na fito, mayaka da dama zasu biyo ni kuma ta haka ne na fito na mika wuya. “A wannan sansanin, zan ce gwamnati da Janar Abdel Ishaq suna yiwa mu da muka mika wuya kokari sosai. Sun lallashe ni sannan sun bani tabbacin cewa idan na ajiye wannan turba da bai da amfani, za a kula da mu. Za a kula da mata da yaranmu sosai.

Labarai Makamanta