Borno: Za Mu Rufe Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Nan Da Wata Biyu – Zulum

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnatin Jihar ta sanar da shirinta na rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke ƙwaryar Maiduguri, babban birnin jihar nan da ƙarshen watan Disamba.

Gwamna Babagana Umara Zulum ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da ‘yan jaridar fadar gwamnati bayan ganawarsa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ranar Juma’a.

Ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon ci gaban da aka samu a harkar tsaro da kuma aikin mayar da ‘yan gudun hijirar garuruwansu na asali.

“Na zo ne na yi wa shugaban ƙasa bayani game da ƙoƙarin da gwamnatin Borno ke yi wajen mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu,” a cewarsa.

“Zuwa yanzu komai yana tafiya daidai, gwamnatin Borno ta gama tsara yadda za a tabbatar an kulle dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri kafin 31 ga watan Disamba.”

Labarai Makamanta