Borno: Tashin Bom Ya Hallaka Mafarauta Bakwai

Akalla mafarauta bakwai ne suka rasu, tare da konewar motoci biyu yayin da suka taka wani bom da kungiyar Boko Haram ta dasa a kan hanya.

Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne ranar Talata, a kauyen Kayamla da ke Karamar Hukumar Jere a Jihar Borno.

Musa Bukar, daya daga cikin ’yan bangar, ya ce “Muna kan sintiri a yankin Kayamla, sai muka ji kara, mun dauka taya ce ta fashe, ashe bom ne muka taka.

“Abun takaici shi ne mun rasa mutum bakwai daga cikin abokan aikimu, sai daya da ya ji rauni. Yanzu haka yana Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ana kula da shi,” cewar Bukar.

‘Yan ta’adda a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun kara ƙaimi wajen kai sabbin hare hare musanman a karshen shekarar nan ta 2020, inda a kusan kullum ake samun kai hare haren na ta’addanci dake hallaka jama’a da dama musamman a Jihar Borno.

An ruwaito daga bakin Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum cewa ba shi da sauran natsuwa ko kwanciyar hankali har sai yaga bayan ayyukan ‘yan ta’adda da suka addabi Jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply