Borno: Rufe Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Ya Bar Baya Da Kura

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar da yawa daga cikin ‘yan gudun hijaran da ke sansanin Bakasssi sun bayyana son komawarsu gida tare da komawa ayyukan nomansu domin samun rufin asiri a maimakon dogaro da tallafi. Sai dai, sun bayyana damuwarsu kan makomar ‘ya’yansu wadanda ke karatu a makarantun gaba da sakandare ba tare da wurin kwana ba.

Gwamnatin jihar Borno a cikin kwanakin nan ta bayyana shirin ta na rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira bayan dawowar zaman lafiya a yankunan da ‘yan Boko Haram suke.

A ranar Asabar, Gwamnan jihar Babagana Zulum ya ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Bakasssi inda ya sanar da mazauna wurin cewa za a rufe shi kuma za a basu dukkan taimakon da ya dace.

A watan Mayun da ya gabata ne gwamnatin ta rufe sansanin ‘yan gudun hijira da aka kafa a kwalejin Mohammed Goni inda aka koma karatu. Masu gudun hijira daga kananan hukumomin Marte, Gwoza, Monguno da Guzamala suna rayuwa a sansanin Bakasssi na shekaru bakwai saboda ta’addanci.

Shugaban mata ‘yan gudun hijira ta karamar hukumar Gwoza da ke sansanin Bakassi, Hauwa Amadu, ta yi maraba da hukuncin gwamnatin jihar na taimakon ‘yan gudun hijira su koma gidajensu. Ta ce da yawa daga cikin iyalan da suka yi gudun hijirar suna rayuwa ne sansanonin saboda basu da yadda za su yi kuma duk wani yunkurin mayar da su gida zai tabbatar da sun samu dogaron kansu ne.

“Ba mu da yadda za mu yi ne, amma zamanmu a sansanin na shekaru 7 saboda kauyukan duk sun lalace ne sakamakon ta’addanci,” Ta ce baya ga Gwoza, Pulka, Izge da wasu tsirarun garuruwa, da yawa daga cikin kauyukan Gwoza babu mutane, wanda hakan ne yasa jama’a daga Amagda, Guduf, Kuranabasa, Wala, Dure da Gasha suke rayuwa a wasu wuararen.

Ta ce shirin gwamnatin jihar na aike wasu ‘yan gudun hijira daga karamar hukumar Gwoza zuwa Maiduguri da Limankara hanya ce ta samar musu isasshen wurin zama da tsaro.

Labarai Makamanta