Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Borno: Mayakan ISWAP Sun Yi Wa Soji Ta’adi

Ƙungiyar mayaƙan ISWAP mai iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin cewa ta kashe mayaƙan sa-kai uku da ke aiki da rundunar sojan Najeriya a Jihar Borno.

Kazalika, ta ce ta yi garkuwa da wasu ma’aikatan agaji na ƙungiyar Red Cross yayin harin da ta ce ta kai ranar Juma’a.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne ciikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram ranar Asabar, tana mai cewa ta kai harin ne a garin Monguno.

A watan Agustan 2020 ne ƙungiyar ta ayyana yaƙi a kan ma’aikatan agaji da ke aiki a Jihar Borno, tana mai zargin su da aiwatar da ayyukan “rusa Musulunci”

Exit mobile version