Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi alkawarin cewa zai fara biyan naira 30,000 ga malaman makaranta a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai Isa Gusau ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce a yanzu haka wasu malaman albashinsu bai gaza naira 11,000 ba sakamakon ayyukan malaman bogi.
Zulum ya fadi hakan ne a ranar Litinin a yayin da yake ƙaddamar da kwamitin hukumar ilimi a matakin farko ta jihar.
Gwamnan ya ce “daya daga cikin manyan matsalolin harkar ilimin firamare a Borno a yau ita ce kula da walwalar malamai. Abin takaici ne a ce har yanzu akwai masu karbar naira 13,000 ko 11,000 a matsayin albashi.
“Ina so na tabbatar da cewa duk da kalubalen da ake fama da shi na tattalin arziki, muna aiki don ganin cewa kowane malami da ya cancanta a Borno yana karbar naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi.”
You must log in to post a comment.