Borno: ISWAP Ta Sace Manyan Ma’aikatan Gwamnati

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wasu Miyagun ƴan ta’addan kungiyar Islamic State in West Africa, ISWAP, sun sace manyan ma’aikatan gwamnatin jihar Borno a ƙalla su biyar.

An sace ma’aikatan ne a ranar Laraba, a lokacin da suka saka ido a kan aikin ginin titin Chibok-Damboa. Lamarin ya faru ne kusa da Wovi, a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Chibok.

Wata majiya ta shaida cewa ɗaya daga cikin ma’aikatan, direba, ya tsira daga harin. Wani babban jami’i ya tabbatar da afkuwar lamarin yana cewa: “Eh, da gaske ne, abin bakin ciki ne kuma abubuwan da ke faruwa a baya bayan nan yana damun mu.

Labarai Makamanta