Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar wasu da ake zargin ‘ya’yan kungiyar ta’addanci ta ISWAP ne sun raba MaĆ™udan kudade ga jama’a Matafiya da ke wucewa ta hanyar Maiduguri zuwa Munguno kafin zuwan ranar da tsofaffin takardun naira za su gama aiki.
Daily Trust ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Mairari da ke kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Munguno a ranar Asabar a karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust a Maiduguri cewa, mambobin ISWAP din sun yi shigar sojoji tare da tuka manyan motocin yaki biyu.
Wani mazaunin yankin mai suna Bakura Ibrahim, yace ‘yan ta’addan sun tsara kansu a karkashin wata bishiya yayin da wasu suka tsaya gefen titi da tsofaffin takardun kudin. “Mun bar Munguno wurin karfe 12 na rana. Yayin da mu ke tunkarar Mairari, mun ga babu sojoji a kan hanya, lamarin da yasa muka saka ayar tambaya.
“Sun tsayar da mu inda suka tambaye mu ko Maiduguri za mu je. Daga nan suka fara baiwa kowanne daga cikin N100,000 amma mun kasa yadda. Sun ba duk wanda ya ke cikin motar mu kirar Golf Volkswagen.”
“Kungiyar ta sanar mana cewa, idan kuna tunanin za ku iya zuwa bankunansu kuma ku canza zuwa sabon kudi, ku je yanzu. Allah ya saka muku albarka a ciki.”
You must log in to post a comment.